9 Mayu 2021 - 14:08
Iran, Ta Yi Watsi Da Zargin Morocco Kan Rura Wutar Rikici A Afrika

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi watsi da zargin da ta ce ba shi da tushe da gwamnatin Morocco ta yi na cewa Iran na aiwatar da ayyukan rura wutar rikici a Arewaci da Yammacin Afrika.

ABNA24 : Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Sa’eed Khatibzadeh a cikin wata sanarwa, ya ce “Saboda gazawarta na magance matsalolin yankunanta, gwamnatin Morrocco, ta sake maimaita zarge-zargen karya da mara tushe kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.”

Ya kara da cewa “Abin takaici ne yadda gwamnatin Morocco, a matsayinta na shugabar kwamitin al-Quds na yanzu (na Kungiyar Hadin Kan kasashen Musulmi (OIC), ta rika goyan bayan Isra’ila da laifufukan da take aikatawa kan a masallacin Kudus.

Wannan dai martanin Iran ne ga furicin da ministan harkokin wajen kasar ta Morocco Nasser Bourita, ya yi a baya baya nan inda ya zargi Iran da cewa ta na aiwatar da ayyukan rura wutar rikici a Arewaci da Yammacin Afrika.

342/